Saturday 24 January 2026 - 23:48
Mai Kare Iyakokin Tunanin Shi'a a Wannan Zamani 

Hauza/ Malaman makarantun Hauza da jami'a a wajen bukin girmama tunanin 'Kalam' na marigayi Ayatullahil Uzma Safi Golpayegani, tare da jaddada irin alfarmar wannan matsayi na wannan marigayi a bangaren kiyaye iyakokin imani, tsarin ilimin tauhidi da kuma amsa shubuhohi na zamani, sun gabatar da shi a matsayin daya daga cikin fitattun malaman Kalam na shi'a a wannan zamani.

A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal-Muslimin Reza Berenjkar a taron tunawa da tunanin Kalam na marigayi Ayatullahil Uzma Safi Golpayegani, wanda aka gudanar a dakin karatu na marigayi Ayatullah Boroujerdi (RA) yayin da yake ishara da fagagen ayyukan wannan marigayin, ya ce: "Marigayi Ayatullah Safi Golpayegani ya rubuta ayyukan ilimi kusan dari, wadanda kusan rabinsu na ilimin Kalam ne, amma fikihunsa da kasancewarsa na zamantakewa da siyasa ya sa wannan bangaren Kalam ya kasa fitowa fili."

Shugaban cibiyar bincike na Ƙur'ani da hadisi ya kara da cewa: "Ayatullah Safi ya ci gaba da samar da ayyuka a fagen ilimin addini tun kafin nasarar juyin juya halin Musulunci har zuwa karshen shekarun rayuwarsa tare da yin bita da kuma buga dayawa daga cikin wadannan ayyuka. Wani muhimmin bangare na littafansa ya yi bayani ne kan tambayoyin addini na mutane ko dai an hada su ta hanyar tambayoyi da amsoshi ko kuma bisa hakikanin al'amuran al'umma."

Haka nan kuma yayin da yake ishara da tafarkin tunani na Ayatullah Safi, Hujjatul Islam wal-Muslimeen Berenjkar ya ce: "Yana amfani da hankali da ruwaya a cikin sukansa (naƙadinsa), kuma daidaiton mu'amalar hankali da wahayi a bayyane yake a cikin ayyukansa. Bayyana Alkur'ani mai girma, hadisai da Nahj al-Balagha, tare da dalilai na hankali, wani nau'i ne na musamman na wannan marja'i a tsarin Kalam."

Yayin da yake jaddada fitar da hujjoji na ilimi daga nassosin addini, ya kara da cewa: "Marigayi Ayatullah Safi ya fayyace kuma ya yi bayanin koyarwar Nahjul Balagha da dama tare da nuna cewa koyarwar littafi da Sunnah ba ruwayoyi ne kawai ba, a'a suna da tushe mai zurfi na hankali."

Shugaban cibiyar binciken Ƙur'ani da Hadisi da yake sukar rashin kulawar da ake ba wa masana ilimin shi'a ya bayyana cewa: "An samu karancin tunawa da marigayi Ayatullah Safi Golpayegani. Idan da irin wannan mutum ya kasance a cikin wasu al'adu ne, da za su saka hannun jari mai yawa don gabatar da bayyana abubuwan da ke tattare da shi, amma abin takaici, a cikin al'adunmu, ana ganin rashin kula da manyan abubuwan da suka gabata.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha